ABNA24 : Jaridar Sudan Tribune ta bayyana cewa kwamitin koli na tsaron kasar ya kara da cewa sojojin kasar Habasha a dayan bangaren suna kama manoma ‘yan kasar ta Sudan wadanda suke aiki a gonakinsu a lardnunan Al-Fashqa Al-Sughra da Al-Fashqa Al-Kubra don korarsu daga yankin.
Jaridar ta nakalto ministan harkokin cikin gida na kasar ta Sudan wanda ya halarci taron kwamitin koli na tsaron kasa, Izzud-Din al-Sheikh ya na cewa sojojin Habasha su na shiga yankunan gabacin kasar Sudan inda suke korar manoma wadanda suke aiki a gonakinsu.
Ministan ya kammala da cewwa sun tattauna matun matsalar ruwan kolin Nilu da kuma matsar ruwa ta Annahdha.
342/